Isa ga babban shafi
Faransa-Coronavirus

Kwararru na cigaba da kiran sake kakabawa Faransawa dokar kulle

Shugaban kungiyar asibitocin Faransa Frederic Valletoux ya bukaci gwamnatin kasar ta dauki matakin sake kakabawa daukacin al’ummar kasar dokar kulle, domin dakile ci gaba da yaduwar cutar Korona.

Wani sashin birnin Paris
Wani sashin birnin Paris REUTERS / Gonzalo Fuentes
Talla

Valletoux ya kuma yi gargadin cewa asibitocin kasar da dama na gaf da gazawa, sakamakon tumbatsar da suka yi da marasa lafiyar da cutar ta Korona ta kwantar.

Kiran na zuwa ne a yayin da aka soma fuskantar baraka tsakanin masana kiwon lafiya da gwamnatin kasar, dangane da matakan yaki da annobar, wadda ta sake barkewa karo na biyu, gami da yaduwa cikin gaggawa.

Sai dai har yanzu babu alamun cewa gwamnatin ta faransa za ta amsa kiraye-kirayen na neman sake killace daukacin al’ummar kasar, bayan da a makon da ya kare yayin jawabi kan halin da ake ciki dangane da yaki da cutar Korona, Firaminista Jean Castex ya nanata cewa gwamnati ba ta da shirin sake kulle kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.