Isa ga babban shafi
Faransa-ta'addanci

Macron ya ce Faransa ba za ta mika wuya ga 'yan ta'adda ba

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasar ba za ta bada kai bori ya hau ba dangane da ayyukan ta’addancin da ake danganta su da addinin Islama bayan da wani dan kasar Tunisia ya daba wa wata ma’aikaciyar 'yan Sanda wuka.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Ian LANGSDON POOL/AFP
Talla

A sakon da ya aike ta kafar twitter bayan kazamin harin da wani dan kasar Tunisia ya kai ta wajen daba wa ma’aikaciyar 'yan Sandan Faransa wuka a wajen birnin Paris, shugaba Emmanuel Macron ya ce a game da yakin da suke da ayyukan ta’addancin da ake dangantawa da addinin Islama ba za su taba bada kai bori ya hau ba.

Majiyoyin bincike sun ce mutumin da ake zargi da kai harin da wuka yayi kabbara, inda ya ce Allahu Akbar kafin daba wa ma’aikaciyar da aka bayyana sunan ta a matsayin Stephanie wuka.

Babban jami‘in gabatar da kara kan laifukan da ke da nasaba da ayyukan ta’addanci a Faransa, Jean-Francoise wanda ofishin ke jagorancin bincike kan lamarin ya ce kalaman da wanda ya kai harin, dan kasar Tunisia wanda tuni aka harbe shi ya yi, ya nuna cewar yana da nasaba da harin ta’addanci.

Hukumar leken asirin cikin gida zata shiga cikin bincike da za’a gudanar, yayin da Faransa ke cikin mataki mafi girma na tsaro saboda kashe kashen da ke da nasaba da ayyukan ta’addancin da ya yi sanadiyar kashe daruruwan mutane a shekarun da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.