Isa ga babban shafi
Faransa

Kotu ta yankewa tsohon sojan Faransa daurin rai da rai kan kisan wata yarinya

Kotu a Faransa ta yankewa wani tsohon sojan kasar hukuncin daurin rai da rai a gidan Yari, bayan samunsa da laifin yin garkuwa da wata yarinya ‘yar shekara takwas tare da kashe ta, lamarin da ya tayar da hankulan mutane a ciki da wajen kasar ta Faransa.

Jami'an tsaro tare da Nordahl Lelandais tsohon sojan Faransa da kotu ta yankewa hukuncin daurin rai da rai kan kisan wata karamar yarinya.
Jami'an tsaro tare da Nordahl Lelandais tsohon sojan Faransa da kotu ta yankewa hukuncin daurin rai da rai kan kisan wata karamar yarinya. © Philippe Desmazes, AFP
Talla

Tsohon sojan Nordahl Lelandais, mai shekaru 39, ya amsa laifin kashe Maelys De Araujo, wadda ta bace a watan Agustan shekarar 2017 daga wani daurin aure a kusa da garin Chambery da ke gabashin Faransa.

‘Yan sanda sun shafe watanni suna neman yarinyar kafin su cafke Lelandais, wanda shi ma bako ne a wurin daurin auren.

Bayan da farko ya musanta zargin, a karshe cikin watan Fabarairun shekarar 2018 tsohon sojan ya kai jami’an tsaron ga gawar yarinyar da ya kashe bayan sace ta da yayi, inda tun daga nan ya dage cewa kuskure aka samu har Maelys ta rasa ranta.

Hukuncin daurin ran da ran da aka yankewa Lelandais ya zo ne ‘yan watanni bayan da aka daure shi kan kashe wani soja, wanda ya lakadawa duka har sai da rai yayi halinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.