Isa ga babban shafi
FARANSA - ALJERIYA

An yi gangamin tunawa da kisan gillar 'yan Aljeriya a Paris

Shekaru sittin bayan, kisan gillar da 'yan sandan Faransa suka yi wa ‘yan Algeria dake zanga -zangar, masana tarihin kasar da kungiyoyin fararen hula da ‘yan siyasa sun yi gangami nuna alhini jiya Lahadi tare da kira ga shugaba Emmanuel Macron da a gudanar da bincike kan wadanda suka aikata aika-aikar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yayin bukin tunawa da 'yan kasar da 'yan sandan Faransa suka kashe yayin zanga-zangar adawa da mulkin mallaka a shekarar 1961.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yayin bukin tunawa da 'yan kasar da 'yan sandan Faransa suka kashe yayin zanga-zangar adawa da mulkin mallaka a shekarar 1961. © AP - Rafael Yaghobzadeh
Talla

Kungiyoyin fararen hula da masana tarihin sunyi gangamin ne domin tunawa da kisan gillar da ‘yan sandan Faransa sukayiwa ‘yan kasar Algeria dake zanga-zangar Adawa da mulkin mallaka da da Faransar ke musu wanda ke cika shekaru 60 da aukuwa.

Emmanuel Macron ya kasance shugaban Faransa na farko da ya halarci bukin na tunawa da kissan gillar, inda ya ajiye Furanni a inda lamarin ya auku shekaru 60 da suka gabata, tare da Allah wadai da abin da ya kira amfani da karfin da ya wuce kima da ‘yan sanda sukayi karkashin jagorancin shugabansu na wancan lokaci a Paris Maurice Papon wanda ya kashe mutane da dama.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yayin bukin tunawa da 'yan kasar da 'yan sandan Faransa suka kashe yayin zanga-zangar adawa da mulkin mallaka a shekarar 1961.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yayin bukin tunawa da 'yan kasar da 'yan sandan Faransa suka kashe yayin zanga-zangar adawa da mulkin mallaka a shekarar 1961. © Rafael Yaghobzadeh, AFP

A yayın ganawa da ‘yan uwan wadanda aka kashe, shugaban Macron yace laifin da ‘yan sanda sukayi a wancan lokaci ba’ abin da kasar zata zata lamunta da shi bane.

To sai dai yayin gamgamin na ranar Lahadi masanan na tarihi da kungiyoyin fararen hula sun ce Allah wadai na shugaba Macron yayi ranar Asabar bai gamsar ba, suna mai kira da a gudanar da bincike, domin a cewarsu shugaban ‘yan sandan wata kila ya samu umurni daga ‘yan siyasa wancan lokaci.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yayin bukin tunawa da 'yan kasar da 'yan sandan Faransa suka kashe yayin zanga-zangar adawa da mulkin mallaka a shekarar 1961.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yayin bukin tunawa da 'yan kasar da 'yan sandan Faransa suka kashe yayin zanga-zangar adawa da mulkin mallaka a shekarar 1961. AFP - RAFAEL YAGHOBZADEH

Kimanin ‘yan kasar Aljeriya masu fafutukar samun ‘yanci dubu 300 zuwa 400 aka kashe a tsakanin shekarar 1954 zuwa 1962,  lamarin da ya Haifa da stamina dangantaka tsakanin Faransa da Aljeriya har zuwa Wannan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.