Isa ga babban shafi
Faransa - Algeria

'Allah wadai' kadai bai gamsar ba akan kissan gillar Aljeriyawa - Masana

A yayin da Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayi Allah wadai da abinda ya kira amfani da karfin da ya wuce kima da ‘Yan Sandan kasar suka yi akan ‘Yan kasar Algeriya dake zanga zangar a shekarar 1961, Masana tarihi da masu fafutuka a kasar sun nuna bacin ransu tare da kira ga shugaban cewa Allah wadai kadai bai wadatar ba.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron © Gonzalo Fuentes, AFP
Talla

A ranar Asabar Shugaba Macron ya yi Allah wadai amfani da karfin da ya wuce kima da ‘Yan Sandan kasar suka yi akan ‘Yan kasar Algeriya dake zanga zangar adawa da kasar Faransa wadda ta yi musu mulkin mallaka abinda yayi sanadiyar kashe mutane da dama.

Yayin ganawa da ‘Yan uwan wadanda aka kashe da masu fafutuka shekaru 60 bayan aukuwar lamarin a birnin Paris, Macron yace laifin da ‘Yan Sandan suka yi a karkashin jagoransu lokacin Maurice Papon ba abin da kasar zata lamunta da shi bane.

A watan Oktobar shekarar 1961 ‘Yan Sandan Faransa suka afkawa ‘Yan kasar Algeria lokacin zanga zangar a birnin Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.