Isa ga babban shafi
Faransa - Algeria

Macron zai halarci bukin tunawa da kisan gillar da aka yiwa Aljeriyawa a Faransa

A wannan Asabar Shugaba Emmanuel Macron zai zama shugaban Faransa na farko da zai halarci bikin tunawa da kisan gillar da 'yan sandan Paris suka yi wa masu zanga-zanga a wani gangamin shekaru 60 da suka gabata kan adawa da mulkin Faransa a Aljeriya a lokacin mulkin mallaka

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yayin wani jawabi a fadar Élysée, 16/09/21.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yayin wani jawabi a fadar Élysée, 16/09/21. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Kafin wannan lokaci an manta da abubuwan da suka wakana a ranar 17 ga Oktoban shekarar 1961, kuma har yazu wanann lokaci ba’asan adadin waɗanda suka mutu a zanga-zangar ba, ko da yake masana tarihi sun yi imanin cewa daruruwan mutane aka kashe.

A wancan lokacin jami’an ‘yan sanda sun rika cilla gawarwakin Aljeriyawa cikin kogin Seine.

An yi  wa Aljeriyawar kisan kare dangin ne a yayin da suka shiga shakara ta bakwai da fafutukar neman  ‘yancinsu daga Turawan Mulkin Mallaka na Faransa.

Bayan da suka shirya zanga-zangar  a shekarar karshe ta yunƙurin Faransa na ci gaba da mallakar Algeria da karfin tsiya, wanda ya zo dai-dai lokacin da masu fafutukar neman yanci suka kaddamar da harin bama-bamai wani yanki na Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.