Isa ga babban shafi
Algeria - Faransa

Aljeriya ta hana jiragen sojan Faransa ketara sararin samaniyarta

A wani mataki dake tabbatar da kara rincabewar dangartakar diflomasaoyya, Gwamnatin Aljeriya ta haramta jiragen sojan Faransa ketare sararin samaniyarta, biyo bayan takaddamar biza da kuma  wasu kalamai da shugaba Emmanuel Macron yayi.

Jirgin yakin Farasa kirar Rafale
Jirgin yakin Farasa kirar Rafale REUTERS/Charles Platiau
Talla

Jiragen Faransa kan yi shawagi akai-akai a yankin Aljeriya don isa yankin Sahel na yammacin Afirka, inda sojinta ke taimakawa wajen yakar masu tayar da kayar baya dake ikirarin Jihadi a wani bangare na aikin Barkhane.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da Algeria ta janye jakadanta dake kasar Faransa, Mohammed Antar Daoud sakamakon rashin jituwa dake kara tsananta a tsakanin kasashen biyu.

Kakakin rundunar, Kanal Pascal Ianni, ya shaida wa AFP cewa "sun samu labarin wannan safiyar wannan Lahadi lokacin da suke shirye-shiryen aike da jirage biyu yankin, kwasan sai suka samu labarin haramcin.

To sai dai Lanni ya ce matakin "bai shafi ayyukansu na tara bayanan sirri a yankin Sahel ba.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da Algeria ta janye jakadanta dake kasar Faransa, Mohammed Antar Daoud sakamakon rashin jituwa dake kara tsananta a tsakanin kasashen biyu.

Kafin daukar matakin na Aljeriya, shugaban Faransa Eammanuel Macron  ya cacaki wata jaridar kasar mai suna Le Monde da ta wallafa labarin cewa Faransar ta yi wa Algeriar Mulkin mallaka cikin Zalunci abin da ya yi wa Algerian zafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.