Isa ga babban shafi
Algeria-Faransa

Yau shekaru 60 da aka yiwa Aljeriyawa kisan gilla a Faransa

Yau ake cika shekaru 60 da al’ummar Algeria suka gudanar da zanga-zanga a birnin Paris na Faransa domin nuna adawa da wata dokar hana su zirga-zirga, lamarin da karkare da kisan kare dangi a wancan lokaci.

Kogin Seine da aka cilla gawarwakin Aljeriyawa a birnin Paris
Kogin Seine da aka cilla gawarwakin Aljeriyawa a birnin Paris Ludovic MARIN AFP/Archives
Talla

Lamarin ya auku ne a shekarar 1961, inda a wancan lokacin jami’an ‘yan sanda suka rika cilla gawarwakin Aljeriyawa cikin kogin Seine.

Wannan kisan kare dangin da aka yi wa mutanen Algeria ya tayar da hankali matuka, inda masanin tarihin nan na Faransa, Emmanuel Blanchard ya bayyana shi a matsayin mafi muni da aka gani a yammacin Turai tun bayan yakin duniya na biyu.

An yi  wa Aljeriyawar kisan kare dangin ne a yayin da suka shiga shakara ta bakwai da fafutukar neman  ‘yancinsu daga Turawan Mulkin Mallaka na Faransa.

Kimanin mutane dubu 30 ne suka gudanar da zanga-zangar a wancan lokacin cikin lumana a babban birnin Paris bayan Kungiyar FLN mai fufutukar samun ‘yancin Algeria ta kira zanga-zangar.

Alkaluma sun nuna cewa, kimanin mutane 200 aka kashe a wancan lokacin, duk da cewa, alkaluman hukumomi sun ce, adadinsu bai wuce uku ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.