Zelensky ya sake yin gargadi game da makaman nukiliyar Rasha
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya nanata gargadin cewa ya kamata duniya ta shirya fuskantar yiwuwar Rasha ta yi amfani da makaman kare dangi na nukiliya a yakin da suke gwabzawa.
Wallafawa ranar:
Zelenskyy ya yi wannan gargadi ne yayin ganawa da manema Labarai a ranar Asabar, inda ya ce suna bukatar tallafin magungunan samar da kariya daga tasirin makaman nukiliya da kuma matsugunan wucin gadin da za su yi amfani da su, domin a cewar sa, Rasha na iya amfani da kowane makami a kowane lokaci daga yanzu.
Shafukan yanar gizo na kafafen watsa labarai na Ukraine guda shida ne suka watsa hirar da shugaba Zelenskyy yayi, sannan kuma fadar gwamnatinsa ta watsa tattaunawar shafinta na Telegram.
Tun a ranar Juma'a, Zelenskyy ya yi gargadin cewa ya kamata duniya ta damu da barazanar da Putin ke yi, yana mai karfafa kalaman daraktan hukumar leken aisiri ta Amurka CIA William Burns.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu