Isa ga babban shafi
Ukraine - Rasha

Ukraine ta zargi Rasha da kai hari kan makaranta a Mariupol

Hukumomin Ukraine sun zargi kasar Rasha da kai harin bam kan wata makaranta dauke da matsugunan mutane 400 dake birni mai tashar ruwa na Mariupol da aka yi wa kawanya, yayin da Moscow ta yi ikirarin cewa ta sake harba makami mai linzami mai gudun walkiya zuwa Ukraine, a karo na biyu kenan ta yi amfani da makamin na zamani mai gudun da ya ninka na sauti sama da 5 cikin sa’a daya a kan makwabciyarta.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky yayin jawabi ta hoton bidiyo, 20/03/2022.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky yayin jawabi ta hoton bidiyo, 20/03/2022. AP
Talla

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce harin Rasha ta kai birnin Mariupol na masu amfani da harshen Rashanci a kudu maso gabashin kasar, inda aka datse hanyoyin sadarwa na tsawon kwanaki, tamkar aikata  laifukan yaki ne, Inda yace dubban sojojin Rasha sun mutu a rikicin.

Yakin da ake yi a Ukraine, wanda shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya kaddamar a ranar 24 ga watan Fabrairu domin kawar da ra'ayin 'yan kasashen yammaci a tsohuwar kasar Soviet, ya haifar da rikicin 'yan gudun hijira mafi girma a Turai tun bayan yakin duniya na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.