Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Tazarar maki 7 tsakanin Madrid da Barca, Inter da Porto sun sha kashi

Maki bakwai ne tsakanin Barcelona da Madrid a La liga, Inter Milan tasha kashi a Seria A, F C porto kuma tasha kashi karo na farko a bana bayan buga wasanni 55 ba tare samun galabarta ba.

Dan wasan Barcelona Lionel Messi rike da kai a lokacin wasansu da Villareal a filin wasa na Madrigal
Dan wasan Barcelona Lionel Messi rike da kai a lokacin wasansu da Villareal a filin wasa na Madrigal REUTERS/Heino Kalis
Talla

Ingila

A Ingila gasar cin kofin FA aka gudanar, inda Liverpool ta doke Manchester United, ci 2-1. Arsenal kuma ta sha da kyar ne hannun Aston Villa ci 3-2.

Spain

A La liga a Spain, wasa tsakanin Barcelona da Villareal an tashi ne babu ci, Real Madrid kuma ta doke Real Zaragoza ci 3-1, hakan ne kuma ya bai wa yaran Mourinho tazarar maki bakwai tsakaninsu da Barcelona.

Kaka da Cristiano da Ozil ne suka zirawa Madrid kwallayenta a raga, amma yaran Guardiola har kammala wasansu kwallo ta kasa fadawa ragar Villareal.

Italiya

A Seria A a Italia, Inter Milan ta sha kashi hannun Lecce ci daya mai ban haushi, kuma wannan ne karon farko bayan buga wasanni 7 ba tare da samun galabarta ba.

AC Milan kuma ta lallasa Cagliari ne ci 3-0. yanzu maki 1 ne kacal tsakanin Milan da Juventus da ke jaogorancin Table. Inda Juve ta doke Udinese ci 2-1 a ranar Assabar.

Faransa

A Faransa Marseille ta doke Rennes ci 2-1.

PSG kuma da ke jagorancin Table ta doke Brest ne ci 1 mai ban haushi, kuma yanzu maki 3 ne tsakanin PSG da Montpellier da ke bi mata a saman Table.

Jamus

A Bundesliga, Bayern Munich ce ke jagorancin Table da yawan kwallaye bayan ta doke Wolfsburg a Munich ci 2-0.

Borussia Dortmund da Schalke 04 suna da maki 40 ne a Table, amma Dortmund ta doke Hoffenheim ne ci 3-1.

Schalke O4 kuma ta lallasa Cologne ci 4-1.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.