Isa ga babban shafi
Wasanni

Ukraine ta mayar da martani ga masu kiran a kaurace wa wasanni a Kasar

PM kasar Ukraine Mykola Azarov ya mayar da martani ga masu kliraye kirayen neman a kaurace wa wasannin gasar cin kofin nahiyar Turai da za a buga a kasar, saboda yadda ake gallaza wa tsohuwar PM Yulia Tymoshenko. PM yace wannan kiran da ake yi, cin fuska ne ga al’ummar kasar ta Ukrain, da za ta karbi bakuncin gasar tare da hadin gwiwar Poland.Wannan gutsuri tsoma ta taso ne, tun bayan da jagorar ‘yan adawan ta Ukrain da ke tsare a gidan yari, ta fara yajin cin abinci, saboda a cewar ta jami’an gidan yarin kasar sun yi ta dukan ta. 

Alamar gasar cin kofin turai na Euro 2012.
Alamar gasar cin kofin turai na Euro 2012. DR
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.