Isa ga babban shafi
Euro 2012

Ingila zata kece raini da Sweden, Faransa zata kara da Ukraine

Ingila da Faransa zasu nemi nasara a wasannin da zasu fafata karo na biyu a gasar cin kofin Turai da ake gudanarwa a kasashen Ukraine da Poland, inda Ingila zata kara da Sweden, Faransa kuma ta kece raini da Ukraine mai masaukin baki.

Samir Nasri dan wasan Faransa wanda ya zira kwallo a ragar Ingila
Samir Nasri dan wasan Faransa wanda ya zira kwallo a ragar Ingila Reuters/Alessandro Bianchi
Talla

Kocin Ingila Roy Hodgson ya bukaci ‘yan wasan shi taka leda domin lallasa Sweden.

A tarihi dai Ingila ba ta samu galabar Sweden ba a gasa, sai dai a yau ba’a maci tuwo ba sai miya ta kare. Amma Jagoran Ingila Steven Gerard yace shi ba wanda ya ke tsoro a Sweden illa Ibrahimovic.

A daya bangeren kuma Ukraine ce mai masaukin baki zata fafata da Faransa. Kuma kocin Faransa Laurent Blanc ya nemi ‘yan wasan shi kaucewa kuskuren da suka yi a wasan su da Ingila.

Kasar Ukraine ce ke jagorancin Rukunin su Ingila da Faransa na D domin Ukraine ta doke Sweden ci 2-1 a karawar farko wasan da Shevshenko ya zira kwallaye biyu a raga.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.