Isa ga babban shafi
Euro 2012

Spain ta lallasa Ireland, Italiya ta yi kunnen doki da Croatia

A gasar cin kofin Turai, Fernando Torres ya wanke kalubalen da ya ke fuskanta na yunwar zira kwallo a raga, bayan ya taimakawa Spain lallasa Jamhuriyyar Ireland ci 4-0, Croatia da ke jagorancin Rukunin C ta yi kunnen doki ci 1-1 da Italiya.

Dan wasan kasar Spain Fernando Torres
Dan wasan kasar Spain Fernando Torres
Talla

A wasan farko da Spain ta fafata da Italiya, saura minti 15 ne a kammala wasan aka sako Fernando Torres a filin wasa, sai dai kuma ana minti hudu da fara wasa ne Torres ya dirka kwallo a ragar Jamhuriyyar Ireland inda daga bisani kuma ya sake zira wata kwallo ana saura minti 20 a kammala wasan.

David Silva da Fabregas ne suka zira wa Spain sauran kwallayenta a ragar Ireland.

Kasar Italia dai yanzu sai ta yi da gaske idan har zata samu damar tsallake wa zagayen Quarter final domin a jiya ta yi kunnen doki ne da Croatia ci1-1.

Croatia tace ta gamsu da sakamakon wasanta da Italia domin a wasan farko ta lallasa Ireland ci 3-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.