Isa ga babban shafi
Euro 2012

Faransa da Ingila sun tsallake, Ukraine da Sweden sun fice

Ingila da Faransa sun tsallake zagayen Quarter Final a gasar Cin kofin Turai, bayan Wayne Rooney ya zira wa Ingila kwallo daya a ragar Ukraine, Faransa tasha kashi ne a hannun Sweden ci 2-0. Amma ta tsallake ne saboda nasarar da Ingila ta samu akan Ukraine.

Andriy Shevchenko yana kallon Terry da rooney suna tabewa bayan Ukraine ta sha kashi hannun Ingila ci 1-0
Andriy Shevchenko yana kallon Terry da rooney suna tabewa bayan Ukraine ta sha kashi hannun Ingila ci 1-0 REUTERS/Yves Herman
Talla

Zlatan Ibrahimovic da Sebastian Larsson ne suka zira kwallo a ragar Faransa, kuma wannan ne ya kawo karshen buga wasanni 23 ba tare da samun galabar Faransa ba karkashin jagorancin Laurent Blanc.

Wannan ne dai karo na farko da Sweden ta samu galabar Faransa shekaru 43 da suka gabata, tun a 1966.

Ingila ta jagoranci teburin Rukunin D kuma wannan ne ya sa zata kauracewa Spain mai rike da kofin gasar a zagayen Quarter Final, domin zata kara ne da Italiya a ranar Lahadi. Kodayake Italia ma ba kanwar lasa ba ce.

A ranar Assabar ne Faransa zata kara da Spain a zagayen Quarter final bayan Faransa ta zo na biyu a teburin rukunin D.

A yau Laraba kafofin yada labaran Birtaniya sun jinjinawa Rooney wanda ya ba Ingila nasara a haskawar Farko a gasar Turai bayan haramta ma shi buga wasanni biyu.

Jaridar Daily Telegraph da Daily Mirror da Daily Mail da kuma Jaridar The sun dukkaninsu sun buga babban labarinsu, suna masu godewa Rooney.

Sai dai Andrei Shevchenko ya yi sallama da bugawa kasar shi wasa bayan Ingila ta fitar da Ukraine a gasar Turai.

A tarihin wasan shi a Ukraine, Shevchenko ya zira wa kasar shi kwallaye 48 a wasanni 111 da ya buga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.