Isa ga babban shafi
Tennis

Djokovic da Azarenka su ne na daya a Duniyar Tennis

Dan wasan Tennis Navak Djokovic shi ne zai rufe shekarar 2012 a matsayin na daya a duniya bayan fitar da jerin matsayin ‘Yan wasan Tennis na duniya bayan ya samu yawan maki 12,920 fiye da dan kasar Switzerland Roger Federer wanda shi ne na biyu da maki 10,265.

Andy Murray yana sunbatar kofin da ya lashe a gasar US Open bayan doke Novak Djokovic a wasan karshe
Andy Murray yana sunbatar kofin da ya lashe a gasar US Open bayan doke Novak Djokovic a wasan karshe REUTERS/Adam Hunger
Talla

Andy Murray na Birtaniya shi ne a matsayi na uku, Rafael Nadal kuma a matsayi na Hudu duk da cewa dan wasan ya kwashe lokaci yana jinya.

A bangaren mata kuma Victoria Azarenka ce ta Belarus a matsayi na daya, Maria Sharapova ta Rasha a matsayi na biyu yayin da Serana Williams ta Amurka a matsayi na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.