Isa ga babban shafi
Tennis

Azarenka da Djokovic sune na daya a Tennis

Victoria Azerenka ce a matsayi na daya a duniyar Tennis a bangaren Mata, Maria sharapova ce da ke bi mata a matsayi na biyu. Serena Willaims ce a matsayi na uku duk da ta lashe kofin Birbane a karshen mako.

Dan kasar Serbia Novak Djokovic
Dan kasar Serbia Novak Djokovic REUTERS/Suzanne Plunkett
Talla

A bangaren maza kuma , Novak Djokovic shi ne na daya a duniyar Tennis, Roger Federer ne ke bi masa a matsayi na biyu. Andy Murray na Birtaniya shi ne na uku yayin da Rafeal Nadal ya kasance a matsayi na hudu bayan ya kwashe lokaci mai tsawo yana jinyar rauni.

David Ferrer da Tomas Berdych da Juan Martin Del Potro da Jo-Wilfried Tsonga na Faransa sune a matsayi na Biyar da na Shida da Bakwai da kuma matsayi na Takwas.
‘Yan wasan Tennis dai na duniya suna ci gaba da shirye shiryen shiga gasar Australian Open, kodayake Rafeal Nadal zai kauracewa gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.