Kim Clijsters ta yi ritaya daga wasan Tennis
Tsohuwar jarumar Tennis ta duniya Kim Clijsters ta yi bankwana da wasan Tennis bayan samun nasara akan Venus Williams a wasan da suka buga domin ritayar ‘yar wasan. Clijsters, ‘yar kasar Belgium ta lashe kofuna 41, kuma ta buga babbar gasar Tennis ta US Open a karo na karshe a watan Agusta ne.
Wallafawa ranar:
A gaban magoya bayanta sama da 13,000, Kim Clijsters mai shekaru 29 ta doke Venus Williams ci 6-3 da ci 6-3.
‘Yar wasar ta taba yin ritaya a shekarar 2007 bayan ta haifi ‘ya Mace. Amma a shekarar 2009 ne ‘yar wasan ta dawo inda kuma ta lashe kofin US Open tare da kare kofinta a shekarar 2010 da kuma kofin Australian Open a shekarar 2011.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu