Casillas da Ramos sun karyata zargin sun bukaci a sallami Mourinho
‘Yan wasan Real Madrid Iker Casillas da Sergio Ramos sun karyata zargin cewar sun nemi Real Madrid ta sallami Mourinho, wannan kuma ya biyo bayan rashin jituwa tsakanin ‘Yan wasan da kocinsu kamar yadda aka ruwaito.
Wallafawa ranar:
A ranar Talata ne Jaridar Marca da ke goyon bayan Madrid ta ruwaito labarin cewar Casillas da Ramos sun bukaci a sallami Mourinho tare da barazanar ficewa kungiyar idan har Real Madrid ba ta sallame shi ba.
Sai dai kuma Casillas da Ramos sun fito sun karyata rahoton tare kare Mourinho daga zargin yana fuskanta matsala da ‘Yan wasan shi.
Copa Del Ray
Barcelona ta tsallake zagayen kusa da karshe a gasar Coper Del Ray bayan doke Malaga da jimillar kwallaye ci 6-4, Bayan a karawar farko kungiyoyin biyu sun tashi wasa ci 2-2.
A zagayen kusa da karshen Barcelona za ta kara ne da Real Madrid, a yayin da kuma Atletico Madrid ta kece raini da Sevilla.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu