Isa ga babban shafi
Wasanni

Usain Bolt ya lashe kyautar Laureus ta Duniya

Dan tseren gudun Jamaica Usain Bolt ya lashe kyutar gwarzon dan wasan Laureus ta bangaren wasanni a Duniya saboda dan wasan ya lashe zinariya guda uku a tseren gudun mita 100 da 200 da tseren gudun mita 400X100 a wasannin Olympics da aka gudanar a birnin London.

Dan tseren gudun kasar Jamaica Usain Bolt rike da kyautar da ya lashe ta Laureus
Dan tseren gudun kasar Jamaica Usain Bolt rike da kyautar da ya lashe ta Laureus Marc Serota/Getty Images For Laureus)
Talla

Wannan ne kuma karo na uku da Bolt ke lashe kyautar karo uku a jere.

Usain Bolt ya samu rinjayen kuri’u fiye da Zakaran kwallon Duniya Lionel Messi da zakaran tseren keken Birtaniya Bradley Wiggins da Mo Farah da kuma dan tseren gudun motoci na Formula one Sebastian Vettel.

Ana gudanar da bukin bayar da kyautar Laureus duk shekara ga bangarori daban daban da suka shahara a harakar wasanni a duniya.

A shekarar 1999 ne, Daimler da Richemont suka kaddamar da kyautar Laureus tare da hadin gwiwar Kamfanin Motoci na Mercedes-Benz da IWC Schaffhausen da Vodafone.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.