Isa ga babban shafi
Seria A

An samu raguwar masu kallon Seria A

Sakamakon wani rahoto da aka fitar a yau Alhamis, yace kungiyoyin da ke taka kwallo a gasar Seria ta Italiya suna kokarin karkato da hankalin masoya kwallon kafa saboda raguwar ‘yan kallo a gasar da kuma matsalar tattalin arziki da ke addabar kasar Italiya.

'Yan wasan Inter Milan a gasar Seria A
'Yan wasan Inter Milan a gasar Seria A REUTERS/Giorgio Perottino
Talla

Wani sakamakon bincike da aka buga yace an samu raguwar masu kallon Seria A da kashi 1.6 tsakanin kakar 2011 zuwa 2012, wanda ke nufin ‘Yan kallo kimanin 200,000 suka kauracewa kallon wasannin Seria A idan aka kwatanta da shekarun baya.

Gasar Seria A dai na cike da matsaloli da suka da cogen wasa da matsalar nunawa bakake wariyar launin fata kuma yanzu gasar Seria A tana kasa ne da gasannin Premier League a Ingila da La liga a Spain da kuma Bundesliga a Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.