Arsenal ta doke Fulham, West Ham ta yi nasara kan Wigan, Bayern ta lallasa Hanovre
A gasar Premier League da ake bugawa a kasar Ingila, a wannan asabar an kara tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasar ga kuma yadda sakamokon ya kasance.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Norwich City ta doke Reading ci biyu da nema, sai Arsenal wadda ta samu nasara a kan Fulham ci 1 da nema, Queens Park Rangers ta sha kashi a hannun Stoke City ci 2 da nema.
Ita kuwa Sunderland ta samu nasarar doke Everton ne ci1 da nema, West Bromwich Albion ta tashi kunnan doki ci1-1 a tsakaninta da Newcastle, West Ham kuwa ta doke Wigan ne ci 2 da nema.
La Liga
A gasar La Liga da ake bugawa a kasar Spain kuwa, ga yadda sakamakon ya kasance.
Granada CF ta yi canjaras da takwararta Valladolid ci 1 kowannensu, yayin da Mojorque ita ma ta tashi kunnan doki da Rayo Vallencano a nan ma ci 1 kowanne.
Bundesliga
A gasar Bundesliga da ake bugawa a kasar Jamus kuwa, a wannan asabar an kara tsakanin wasu manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasar, ga kuma yadda sakamakon wasu daga cikin wasannin ya kasance.
Eintract ta lallasa Schalke 04 ci 1 da nema, sai Dortmund wadda ta samu nasara a kan Mayence ita ma ci 2 da nema, yayin da Hanovre ta sha mummunan kashi a hannun ‘yan wasar Bayern Munich ci 6 da 1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu