Isa ga babban shafi
Wasanni

Mourinho ya ce zai bar Real a karshen kakar bana

Mai koyar da ‘yan wasan Real Madrid, Jose Mourinho yace da wuya ya ci gaba da aiki a matsayin kocin kungiyar, a kakar wasanni mai zuwa, inda yace ya fi son ya je inda ake kaunar shi, dama an dade ana hasashen hakan. Ko a baya sai da Mourinho, wanda dan asalin kasar Potugal ne, ya yi ta bayana yiwuwar komawar shi kasar Ingila.Wasu suna cewa watakila ya koma Chelsea, inda ya baro a shekarar 2007, bayan rashin jituwar da ta shiga tsakanin shi da mai kulob din, Roman Abramovich. Sai dai kuma har yanzu masoya kungiyar ta Chelsea suna kaunar shi, ganin irin nasarorin da ta samu a zamanin da yake rike da kungiyar.Za a iya cewa watakila faduwa ta zo daidai da zama ke nan, don kuwa manajan Chelsea mai ci Rafael Benitez, yace a karshen wannan kakar wasannin zai yar da kwallon mangwaro, don ya huta da kuda, don kuwa zai yi adabo da Stamford Bridge din. 

Jose Mourinho ya kusa yin "Adabo" da Real
Jose Mourinho ya kusa yin "Adabo" da Real Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.