Isa ga babban shafi
Champions League

Za’a fitar da gwani tsakanin Kungiyoyin Jamus guda biyu

A gobe Assabar za’a kwashi kallo a filin wasa na Wembley a Ingila inda kungiyoyin Jamus guda biyu Bayern Munich da Borussia Dortmund zasu kara a wasan karshe na gasar zakarun Turai.

Tambarin kungiyoyin Jamus Bayern Munich da Borussia Dortmund
Tambarin kungiyoyin Jamus Bayern Munich da Borussia Dortmund
Talla

Wasan gobe mataki ne na farfado da gasar Bundesliga ta Jamus inda a daukacin kasashen Turai, aka fi samun saukin farashin tikitin shiga kallon wassani.

Akalla ana haska wasanni Bundesliga a kasashe 150 amma gasar ba ta kamo kafar Premier ta Ingila ba idan aka yi maganar samun kudi a filayen wasa.

Kungiyoyin ingila dai suna samu karfi daga attajiran kasashe irinsu Rasha da yankin Asia da Gabas ta tsakiya wanda hakan yasa aka samu kungiyoyi hudu da suka taba lashe kofin gasar zakarun Turai har guda uku, Liverpool da Manchester United da kuma Chelsea.

A bana Bayern Munich da Borussia Dortmund ne suka yi waje da manyan kungiyoyin Spain guda biyu Barcelona da Real Madrid wanda hakan ke nuna kungiyoyin Bundesliga sun fara farfadowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.