Isa ga babban shafi
Champions League

Dubarar Gudu da kwallo ta kawo karshen tabe tabe a filin wasa

Kungiyoyin Jamus guda biyu, Borussia Dortmund da Bayern Munich sun mamaye kanun labarai a Nahiyar Turai bayan sun lallasa manyan kungiyoyin Spain guda biyu Real Madrid da Barcelona a gasar Zakarun Turai zagayen kusa da karshe.

Dan wasan Bayern Munich Arjen Robben ya sha gaban 'Yan wasan Barcelona a gasar zakarun Turai da kungiyoyin biyu suka buga a zagayen kusa da karshe.
Dan wasan Bayern Munich Arjen Robben ya sha gaban 'Yan wasan Barcelona a gasar zakarun Turai da kungiyoyin biyu suka buga a zagayen kusa da karshe. REUTERS/Gustau Nacarino
Talla

Borussia Dortmund da Bayern Munich su ne kungiyoyin da za su buga wasan karshe a filin wasa na Wembley a ranar 25 ga watan Mayu a kasar Ingila.

Borussia Dortmund ta tsallake ne da jimillar kwallaye ci 4-3 a ragar Real Madrid, a yayin da kuma Bayern Munich ta tsallake da jimillar kwallaye 7-0 a ragar Barcelona.

Yadda Bayern Munich ta yi waje da Barcelona da Arsenal a bana ta hanyar dabarar gudu da kwallo ya nuna illar dabarar tabe tabe a filin wasa. Bayern Munich ta kauce wa yin amfani da salon yin yanke inda da yi amfani da karfi wajen gudu da kwallo.

A bana, Bayern Munich tana neman lashe kofuna uku ne bayan ta lashe kofin Bundesliga kuma za ta buga wasan karshe a kofin Jamus da Gasar Zakarun Turai.

Wannan ne karo na uku da Bayern Munich ke tsallakewa zuwa buga wasan karshe cikin shekaru hudu a jere.

Wannan ne karo na farko da kungiyoyin Jamus guda biyu za su buga wasan karshe a gasar Zakarun Turai. Kuma Bayern Munich tana neman zama kungiya ta farko daga jamus da za ta lashe kofuna uku a shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.