Isa ga babban shafi
Tseren Keke

An watsa wa Cavendish Fitsari a Tour de France

Kungiyar Omega Pharma ta tabbatar da labarin ‘Yan kallo sun watsawa dan tseren kekenta Mark Cavendish Fitsari a dai dai lokacin da ake tseren keke mataki na 11 a gasar tseren keke ta Tour de France da ake gudanarwa a Faransa.

Mark Cavendish a tseren  Keke na Tour de France
Mark Cavendish a tseren Keke na Tour de France REUTERS/Bogdan Cristel
Talla

Akwai dai zargi da ake wa Mark Cavendish game da hadarin da aka samu a mataki na 10 inda ‘Yan tseren keken suka yi tutsu, kuma ana ganin ‘Yan kallon sun hasala ne a tseren na Kilimota 33 mataki na 11.

Mark Cavendish ya tsallake hukunci bisa hadarin da ya faru a jiya inda Kittel dan tseren keken Jamus ya lashe.

Duk da dai Mark Cavendish ya nemi afuwa amma ‘Yan kallo sun huce hushinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.