Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Gareth Bale ya shiga jerin 'yan takarar kyautar Ballon d’or

Sabon dan wasan Real Madrid Gareth Bale ya samu shiga jerin ‘yan wasan 23 da aka tsamo domin neman shiga gasar lashe kyautar gwarzon dan wasan shekarar 2013 ta Ballon d’or.

Sabon dan wasan Real Madrid Gareth Bale a lokacin da aka gabatar da shi
Sabon dan wasan Real Madrid Gareth Bale a lokacin da aka gabatar da shi REUTERS/Rebecca Naden
Talla

Cikin jerin sunayen akwai ‘yan wasa irinsu Lionel Messi na Barcelona wanda ya lashe kyautar sau hudu a jere da Cristioano Ronaldo na Real Madrid da kuma Zlatan Ibrahimovic na PSG har ila yau da Robin Van Persie na Manchester United da kuma Frank Ribery na Bayern Munich.

Yanzu haka kungiyar Bayern Munich tafi yawan ‘yan wasa a jeri sunayen da aka fitar lamarin da ya shugaban kungiyar kungiyar Karl –Heinz Rummernigge ya ce hakan na nuni da cewa Bayern ta yi fice a wasan kwallo.

Yaya Toure wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Nahiyar Afrika ya samu shiga, wanda hakan ke nufin shine dan wasan kadai da zai yi takarar daga wajen Nahiyar Turai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.