Man. U. ta lallasa Arsenal da ci 1-0
Mai horar da ‘yan wasan Manchester United David Moyes ya ce har yanzu akwai sauran tafiya a gabansu duk da cewa sun doke Arsenal dake jagorantar teburin gasar premier da ci 1-0 a jiya lahadi. Robin Van Persie ne ya zirawa Man. U. kwallonta.
Wallafawa ranar:
Tun fara wannan kakar wasa, Manchester dai ta sha kashi a hanun Liverpool, da Manchester City da kuma Westbrom Albion.
A sauran sakamakon wasannin da aka buga a karshen mako a gasar ta premier, Newcastle ta doke Tottenham da ci 1-0, haka itama Sunderland ta lallasa Man City da ci 1-0 yayin da Swansea da Stoke suka ta shi da ci 3-3.
Chelsea kuwa ta yi kunnen doki ne da Westbrom da ci 2-2, Liverpool kuwa ta lallasa Fulham da ci 4-1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu