Isa ga babban shafi
Bundesliga

Dortmund ta sha kashi a hannun Bayern

Bayern Munich ta samu kwarin gwiwar kare kofinta na Bundesliga a bana bayan a karon farko ta samu sa’ar lallasa abokiyar hamayyarta Borussia Dortmund ci 3-0 tsawon shekaru hudu tana shan kashi a gasar a karawa tsakanin kungiyoyi biyu da ake wa kirari da Clasico ta Jamus.

Thomas Mueller na Bayern Munich yana murnar zira kwallo a ragar Borussia Dortmund  a gasar Bundesliga
Thomas Mueller na Bayern Munich yana murnar zira kwallo a ragar Borussia Dortmund a gasar Bundesliga REUTERS/Ina Fassbender
Talla

Tsohon dan wasan Dortmund ne Mario Goetze ya fara bude raga ana minti 66, daga bisani kuma Arjen Robben da Thomas Mueller suka zira sauran kwallayen ana saura minti biyar a kammala wasan.

Wannan ne karon farko da Bayern Munich ta samu nasara akan Dortmund a karawar kungiyoyin biyu sau bakwai, wanda ya ba Bayern nasarar buga wasanni 38 ba tare da samun galabarta ba a bana.

Bayern Munich ce ke jagorancin teburin gasar Bundesliga da tazarar maki 4 tsakaninta da Bayer Leverkusen, kungiyar da ta karbe wa Dortmund matsayi na biyu bayan ta sha kashi a karshen mako.

A lokacin da ya ke zantawa da manema labarai kocin Bayern Munich yace akwai cikin ‘Yan wasan shi da ke kwarmata wa ‘Yan jarida dubarun shi tare da gargadin zai dauki mataki.

Pep Guardiola yace idan har ya gono ko wanene zai mayar da shi saniyar ware ba zai sake buga masa wasa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.