Kotu ta yankewa shugaban Bayern hukuncin zaman gidan yari
Wata kotu a kasar Jamus ta yankewa Shugaban kungiyar kwallon kafar Bayern Munich Uli Hoeness, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru uku da rabi, bayan da aka same shi da laifin kaucewa biyan kudaden haraji na miliyoyin daloli.
Wallafawa ranar:
Dan shekaru 62, Hoeness ya amince da cewa ya kaucewa biyan akalla kudi sama da miliyan 37 na dalar Amurka, inda ya boye su a wasu bankunan dake kasar Switzerland cikin shekaru da dama.
An dai kyale Hoenes ya fice daga kotun bayan kammala sharia’r, inda aka bashi mako daya ya yi shawara ko zai daukaka kara kan wannan hukunci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu