Faransa ta fara gasar cin kofin duniya da kafar dama
Kasar Faransa ta lallasa takwararta Hounduras da ci 3-0 bayan da suka kara a wasansu na farko a gasar cin kofin duniya da ake yi a kasar Brazil.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Dan wasan Faransa Karim Benzema ne ya zira kwallaye biyu daga cikin kwallaye uku, wanda hakan ya sa yana da kwallaye 23 ke nan da ya zirawa kasarsa.
Masu sharhi kan kwallon kafa na bayyana cewa haskarwar da Benzema ya yin a da nasaba da rashin zuwan Frank Ribery gasar.
Benzema ya zira kwallo ta farko wacce aka yi amfani da fasahar tantance sigar kwallo raga kamin a fayyace sahihancin kwallon a karon farko a gasar kasa da kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu