Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

An kashe kudi a kasuwar ‘Yan wasa fiye da shekaru 5

Wani sakamakon binciken na kasuwar cinikin ‘Yan wasa yace kungiyoyin kwallon kafa a Turai sun kashe kudi wajen cefanen ‘Yan wasa a bana da kusan kashi 16 fiye da shekaru biyar da suka gabata. Cibiyar CIES da ke nazari akan kwallon kafa a kasar Switzerland tace Manchester United da PSG sun kashe Miliyoyian daloli musamman wajen mallakar Di Mari da David Luiz.

Radamel Falcao da Manchester United ta saya daga Monaco
Radamel Falcao da Manchester United ta saya daga Monaco DR
Talla

Gasar Premier ce dai aka bayyana akan gaba wajen kashe kudade inda kungiyoyin 20 da ke taka kwallo a gasar suka kashe kudi Fam Miliyan £835, kuma Manchester United ce a sahun gaba.

Sai kuma Gasar La liga a matsayi na biyu wajen kashe kudi inda kungiyoyin gasar suka kashe jimillar kudi sama da dala miliyan 700, kuma Real Madrid da Barcelona ne kan gaba wadanda suka zuba kudi suka saye Luis Suarez da James Rodriguez.

Sai kuma sauran gasannin Serie A da aka kashe kudi dala Miliyan 450, sai Bundesliga ta Jamus da aka kashe kudi dala Miliyan 415 da kuma Ligue 1 a Faransa da aka kashe kudi Dala Miliyan 165.

Kuma wadannan manyan gasannin guda biyar nan ne aka fi musayar ‘Yan wasa fiye da sauran wasannin a kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.