Isa ga babban shafi
Zakarun duniya

Real Madrid ta doke Cruz Azul a Morocco

Real Madrid mai rike da kofin zakarun Turai ta kai zagaye na karshe a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyoyin duniya da ake gudanarwa a Morocco bayan ta lallasa Cruz Azul ta Mexico ci 4 da 0.

Cristiano Ronaldo da Karim Benzema da Bale a Morocco
Cristiano Ronaldo da Karim Benzema da Bale a Morocco REUTERS/Youssef Boudlal
Talla

Sergio Ramos da Karim Benzema da Garreth Bale da Isco ne suka zirara wa Madrid kwallayenta a raga, inda yanzu Real Madrid ta buga wasanni 21 ba tare da samun galabarta ba.

A yau Laraba ne San Lorenzo ta Argentina za ta fafata da Auckland City ta New Zealand. Cikinsu duk kungiyar da ta samu nasara ita za ta hadu da Real Madrid a karawar karshe.

Copa del Ray

A gasar Copa del Ray ta Spain, Barcelona ta casa Huesca da ke mataki na uku a League ci 8 da 1, Pedro ne ya zirara kwalaye uku yayin da Sergi Roberto da Andres Iniesta da Adriano, da Adama Traore da Sandro suka jefa sauran kwallayen a raga.

Yanzu Barcelona ta shiga zagaye na biyu, kamar yadda tuni Real Madrid da Sevilla da Valencia suka tsallake.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.