Isa ga babban shafi
Jamus

Dortmund ta doke Bayern Munich

Borussia Dortmund  ta samu sa’ar Bayern Munich a bugun Fanariti a yayin da Kungiyoyin biyu suka yi kunnen doki 1 da 1 a zagayen dab da na karshe a gasar lashe kofin Jamus. Bayern Munich ta barar da dukkanin kwallayen da ta buga a Fanariti.

'Yan wasan Borussia Dortmund a lokacin da suka doke Bayern Munich a gasar lashe kofin Jamus
'Yan wasan Borussia Dortmund a lokacin da suka doke Bayern Munich a gasar lashe kofin Jamus REUTERS
Talla

Dortmund da ke fuskantar kalubale a Bundesliga yanzu ta kawo karshen Burin Bayern Munich na lashe kofi uku a bana bayan ta lashe kofin Bundesliga a ranar lahadi.

A Larabar makon gobe ne dai Bayern Munich za ta hadu da Barcelona a gasar zakarun Turai, sai dai rahotanni sun ce har zuwa lokacin Robben da Lewandowski ba za su zasu samu damar buga wasan ba saboda rauni.

Wannan ne dai karo na uku cikin shekaru hudu da Dortmund ke kai wa zagayen karshe a gasar lashe kofin Jamus karkashin jagorancin Jurgen Klopp wanda tuni ya bayyana cewa zai fice kungiyar a karshen kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.