Isa ga babban shafi
Tennis

Djokovic zai fafata da Murray

Novak Djokovic zai kece raini da Andy Murray a fafatawar daf da na karshe a gasar Roland Garros da ake ci gaba da gudanarwa a Faransa. Wannan ne karo na 27 da fitattun ‘Yan wasan na duniya ke fafatawa a tarihin rayuwarsu a Tennis.

Novak Djokovic ya doke Rafael Nadal a Roland Garros
Novak Djokovic ya doke Rafael Nadal a Roland Garros Reuters/Jean-Paul Pelissier
Talla

A daya bangaren, Stanilas Wawrinka zai kara ne da Jo-Wilfied Tsonga wasan na kusa da karshe a yau Juma’a.

Wawrinka wanda ya lashe kofin Australian Open a bara shi ne ya yi waje Roger Federer a kwata Fainal yayin da Tsonga ya doke Tomas Berdych.

Ana ganin dai Djokovic na iya lashe gasar a bana bayan ya yi waje da Rafael Nadal a zagayen kwata fainal wanda ya lashe kofin Roland Garros sau 9.

Djokovc na harin lashe kofin gasar ne karo na farko a Paris, bayan sau uku yana kai wa zagayen karshe ba tare da samun nasara ba.

Sai dai kuma Andy Murray na Birtaniya shi ma ba kanwar lasa ba ne domin sai Djokovic ya yi da gaske.

A gobe Assabar ne za a yi fafatawar karshe a bangaren mata inda Serena Williams ke harin lashe kofin Gram Slams karo na 20 idan ta doke Lucie Safarova.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.