Isa ga babban shafi
FIFA

G7- An bukaci tsafta a FIFA

Shugaban Kasar Amurka Barrack Obama ya bayyana cewa , yana da matukar muhimmaci hukumar kwallon kafa ta duniya ta tabbatar da tsafta a harkan wasanni a duniya

Sepp Blatter, shugaban FIFA mai murabus
Sepp Blatter, shugaban FIFA mai murabus REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

Obama ya fadi haka ne a taron G7 da manyan kasashen duniya masu arzikin masana’antu ke gudanarwa a birnin a Kasar Jamus bayan jarida sun masa tambaya game da badakalar cin hanci da rashawa ta da dabaibaye hukumar ta FIFA, lamarin kuma ya yi sanadiyar murabus din Sepp Blatter a matsayin shugaban hukumar.

Shugaba Obama ya kara da cewa, yana da muhimmaci a fahimci cewa, kwallon kafa wasa ne kuma tamkar harkar kasuwanci ne da ake samun kudade, Kana wata hanya ce ta samarwa kasa martaba da jama’ar dake cikinta, don haka ya zamaa tilas a gudanar da al-amura a hukumar FIFA cikin tsafta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.