Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA ta cimma yarjejeniyar sirri kan gasar 2018 a Rasha

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Sepp Blatter ya bayyana cewa sun cimma yarjejniya a boye dangane da bai wa Rasha damar daukan bakwancin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018 kafin a kada kuri’ar amince wa da haka. 

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Sepp Blatter.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Sepp Blatter. Reuters/Arnd Wiegmann/
Talla

Blatter wanda ya caccaki kasashen Ingila da Amurka game da badakalar cin hanci da rashawa da ta addadi hukumar kwallon kafa ta duniya ya ce, kwamitin zartarwa na FIFA mai kunshe da mutane 22, sun yanke shawarwari guda biyu a shekera ta 2010, inda suka amince su kai gasar ta cin kofin duniya kasar Rasha a shekara ta 2018 sannan kuma su koma kasar Amurka a shekara ta 2022.

A cewar Blatter, da a ce Amurka ta yi nasarar samun izinin daukan bakwancin gasar a shekara ta 2022, da yanzu kawai hankula sun karkata ne akan batun damar da aka bai wa Rasha na daukan bakwancin gasar, amma ba akan matsalar da hukumar kwallon kafa ta duniya ke fama da it aba.

Kalaman Blatter dai sun tinzira shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila, Greg Dyke, inda ya ce zai gudanar da bincike game da dawo da kudaden da aka kashe da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 32 bayan kasarsa ta rasa izinin daukan bakwancin gasar ta cin kokfin duniya a shekara ta 2018

.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.