Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Guinness ya karrama Lewandowski

Kamfanin giya na Guinness ya karrama dan wasan kungiyar Bayern Munich Robert Lewandowski bayan ya kafa wani tarihi a duniya a fagen kwallon kafa.

Robert Lewandowski ya karbi takardun sheda guda hudu daga Kamfanin Guinness
Robert Lewandowski ya karbi takardun sheda guda hudu daga Kamfanin Guinness @homebayern
Talla

Lewandowski cikin mintuna 8 ya jefa kwallaye 5 a raga a wasan da Bayern Munich ta doke Wolfsburg ci 5 da 1 a ranar 22 ga watan Satumba.

A jiya Litinin ne kuma Kamfanin Guinness ya karrama dan wasan da takardun sheda guda hudu, da farko a matsayin wanda ya jefa kwallaye uku cikin kankanin lokaci minti 3:22, sannan cikin minti 5:42 ya jefa kwallaye hudu, haka kuma cikin minti 8 ya jefa kwallaye 5.

Sannan shi ne dan wasa na farko a tarihin kwallon kafa a Jamus wanda yana benci aka sako shi ya jefa kwallaye biyar.

Bayan karbar kyautukan Lewandowski yace zai yi kyauta da takalmin kwallon da ya ci wadannan kwallaye a matsayin tallafi.

Kwallayen da Lewandowski ya jefa a ragar Wolfsburg cikin mintina 8

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.