An bankwado cogen wasa a Tennis
Badakalar cogen wasa ta kunno kai a wasan Tennis bayan Novak Djokovic zakaran Tennis din na duniya ya kwarmata cewa an taba tuntubarsa da kudi domin ya yi coge.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka kuma ‘yan wasan na Tennis da dama na ci gaba da fasa kwai a harakar ta cogen wasa.
Hukumomin Tennis da ‘yan sanda sun sa ido a wasannin Australian Open da ake gudanarwa a Melbourne yanzu haka kan badakalar cogen wasan da aka fara fallasawa a wasan.
Wannan dai sabon abu ne a sha’annin Tennis, yayin da ake fama da matsalar shan abubuwa masu sa kuzari a harakar wasanni.
Novak Djokovic ya ce a lokacin kuriciyarsa a wasan Tennis an taba ma shi tayin kudi dala dubu dari biyu domin ya yi coge a Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu