Isa ga babban shafi
Wasanni

Van Gaal na son Rooney ya kafa tarihi a Manchester United

Kocin Manchester United Louis Van Gaal ya yi fatan cewa keften dinsa Wayne Rooney zai kafa tarihi a wannan kakar a matsayin wanda ya fi zura kwallaye a tarihirin Manchester United.

Wayne Rooney na Manchester United
Wayne Rooney na Manchester United
Talla

Van Gaal dai na burin ya ga cewa Rooney ya zarce Sir Bobby Charlton, wanda har yanzu ba a samu dan wasan Manchester United ba da ya ci wa kungiyar kwallayen da suka kai yawan nasa, inda ya zura kwallaye 249.

A yanzu dai Rooney na bukatar zura kwallaye biyar a raga kafin ya kamo Charlton kuma a jiya ma sai da ya ci wa Manchester United kwallo guda a wasan da ta lallasa Stoke City ci 3-0 a gasar Premier ta Ingila.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.