Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya fice daga dakin taro

Gwarzon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Madrid, Christiano Ronaldo ya fice daga dakin taron manema labarai da aka gudanar a jiya Talata bayan an tambaye shi a game da kwallayen da ya zura a wasannin da kungirsa ta yi a waje a cikin wannan kakar.

Cristiano Ronaldo na Real Madrid
Cristiano Ronaldo na Real Madrid Facebook Fifa Ballon d'Or
Talla

Ronaldo dai mai shekara 31 da haihuwa ya zura kwallaye 32 cikin wannan kakar amma tun a ranar 29 ga watan Nuwamban bara raban da ya ci kwallo a waje .

A martanin da ya mayar, dan wasan ya ce, wanene ya ci yawan kwallaye fiye da shi a waje tun lokacin da ya koma kasar Spain da taka leda.

Ronaldo dai shi ya fi yawan kwallaye a gasar cin kofin zakarun Turai, inda ya zura kwallaye 88 a cikin wasanni 121.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.