Barcelona ta kai wasan karshe na Copa del Rey
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta samu nasarar tsallkawa zagayen karshe a gasar Copa del Rey bayan ta doke Valencia da ci 8-1.
Wallafawa ranar:
Ko da yake a jiya ne kungiyoyin biyu suka yi wasa a zagaye na biyu inda suka tashi 1-1 amma a wasan zagayen farko Barcelonan ta lallasa Valencia da 7-0.
Wannan sakamakon dai ya nuna cewa ba a doke Barcelona ba a wasanni 29 da ta yi.
Yanzu haka dai ana sa ran za ta hadu ne da Sevilla ko kuma Celta Vigo a wasan karshe na gasar Copa del Rey, sai dai an fi kyautata zaton da Sevilla za ta hudu, lura da cewa Sevilla ta casa Celta Vigo da ci 4-0 a wasansu na farko.
A yau Alhamis ne Sevilla za ta kara da Celta Vigo a zagaye na biyu na wasansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu