Isa ga babban shafi
Wasanni

Mourinho zai koma Manchester United

A yau laraba, jaridun Birtaniyya da suka da Daily Mail da Daily Star da Daily Mirror har ma da Daily Telegraph sun rawaito cewa, tsohon kocin Chelsea Jose Mourinho zai gaji Louis Van Gaal a matsayin mai horar da Manchester United a karshen wannan kakar wasannin. A cewar Jaridun, Mourinho ya fada wa abokansa da makusantansa cewa an riga an cimma yarjejeniyar zamansa a Old Trafford, sai dai ba a bayyana sunayen wadanda ya zanta da su ba kan wannan batu.A wata hira da aka yi da shi a cikin makon daya gabata, kocin, dan asalin kasar Portugal kuma mai shekaru 53 ya bayyana cewa, nan ba da jimawa ba zai koma horar da wata kungiyar kwallon kafa amma in san samu ne ta kasance a Ingila.Mourinho dai ya horar da Real Madrid da Inter Milan har ma da Porto yayin da a watan Disamban bara, Chelsea ta raba gari da shi.                  

Jose Mourinho
Jose Mourinho Reuters/John Sibley
Talla

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.