Isa ga babban shafi
Wasanni

PSG ta kai matakin gaba a gasar Faransa

A jiya Laraba an yi wasa  tsakanin PSG da Lyon a gasar cin kofin Faransa, inda PSG din ta samu nasara da ci 3-0 kuma Zlatan Ibrahimovic ne ya zura kwallaye biyu cikin minti hudu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci yayin da Agrien Rabiot ya zura tasa kwallon a minti na 75.

Dan wasan PSG Zlatan Ibrahimovic da ya zura kwallaye biyu a karawarsu da Lyon.
Dan wasan PSG Zlatan Ibrahimovic da ya zura kwallaye biyu a karawarsu da Lyon. REUTERS/Andreas Hillergren
Talla

Yanzu haka PSG ta samu nasarar kai wa matakin wasan dab da na kusan karshe wato quarter final.

Kungiyar PSG dai ba ta taba shan kayi ba a dukkannin wasannin da ta yi tun bayan da Real Madrid ta casa ta a farkon watan Nuwamban bara a gasar cin kofin zakarunn Turai kuwa wasanni 21 ta buga, inda ta yi canjaras a guda daya kacal.

Ana sa ran, PSG za ta hadu da Saint Etienne wadda ita ma ta kai zagaye na gaba bayan ta doke Troyes da ci 2-1 a jiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.