Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi na Barcelona ya kafa tarihi a La Liga

Gwarzan dan wasan Barcelona Lionel Messi ya zama dan wasa na farko a tarihi da ya zura kwallaye 300 a gasar La Liga yayin da ya saka kwallaye biyu a ragar Sporting Gijon a wasan da suka yi a jiya Laraba, inda suka ta shi 3-1.

Lionel Messi da abokinsa Neymar
Lionel Messi da abokinsa Neymar Reuters/Albert Gea
Talla

Messi ne dai ya fara zura kwallo a fafatawar ta jiya kafin daga bisani Carlos Castro na Sporting Gijon ya farke .

Sannan Messin ya sake saka wata kwallon a ragar Sporting Gijon bayan Luiz Suarez ya garo masa ita.

Suarez din ne ya zura kwallo ta uku yayin da a yanzu Barcelona ke jan ragama a teburin gasar ta La Liga.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.