Isa ga babban shafi
Najeriya

El Kanemi za ta soma a wasa a Maiduguri

A karon farko kungiyar El Kanemi Warriors za ta buga wasan farko filinta da ke Maiduguri, bayan kauracewa filin tsawon shekaru uku saboda rikicin Boko Haram.

Kungiyar El Kanemi ta Maiduguri
Kungiyar El Kanemi ta Maiduguri npfl.ng
Talla

El Kanemi za ta karbi bakuncin Shooting stars ne a ranar Lahadi, kamar yadda kakakin kungiyar Anthony Obaseki ya tabbatar bayan sun samu damar buga wasan a Maiduguri.

El Kanemi na fatar magoya bayanta zasu shiga kallon wasan domin samun nasara.

Tuni dai tawagar kungiyar Shooting Stars ta kama hanya zuwa Maiduguri domin karawa da El Kanemi.

El Kanemi dai na matsayi na 14 ne a teburin gasar Firimiya ta Najeriya da maki 11 a wasanni 10 da aka buga.

Rikicin Boko Haram dai ya sa mutane da dama sun fice Jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.