BOKO HARAM: Mutane 22 sun Mutu a Borno
Akalla mutane 22 suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da aka kai cikin Masallacin kauyen Umarari da ke Jihar Borno, a dai-dai lokacin Sallar Asuba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A cewar hukumomi Jihar ta Borno harin Umarari dake da tazaran kilomita 5 daga birnin Maiduguri ya kuma jikkata wasu 32.
Wannan harin shine irin sa na farko a Borno tun bayan harin da aka kai sansani ‘yan gudun hijira dake Dikwa tare da kashe mutane 50.
A cewar wani Jami’an rundunar sa kai ta fararan kaya Alhaji Danbatta, maharan su biyu, sun kutsa kai cikin masallaci a dai-dai lokacin da ake jam’in Sallah kana ya tada bam din dake jikinsa.
Jihar Borno dake yawaita fuskantar hare-haren Mayakan Boko Haran, Rundunar sojin Najeriya na ikirarin kakkabe mayakan daga kauyukan jihohin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu