Isa ga babban shafi
Wasanni

Ban taba murna ba kamar wannan lokacin- Hodgson

Mai horar da tawagar kwallon kafa ta Ingila, Roy Hodgson ya bayyana murnarsa matuka akan kwallon da dan wasansa Daniel Strurridge ya zura a ragar Wales a karawar da suka yi a jiya a gasar cin kofin kasashen Turai da ake yi a Faransa.

Roy Hodgson, mai horar da tawagar kwallon kafa ta Ingila
Roy Hodgson, mai horar da tawagar kwallon kafa ta Ingila Reuters/Carl Recine
Talla

Wannan kwallon da Sturridge ya jefa, ita ce ta bai wa Ingila nasara akan Wales har suka tashi 2-1.

Hodgson ya ce, ya dade rabon da ya yi murna sosai saboda wata kwallo da aka wurga a raga kamar yadda ya yi a lokacin da Sturridge ya jefa wannan kwallon a minti na 91.

Kasar Wales ce dai ta fara zura kwallo a ragar Ingila ta hannnun Gareth Bale bayan sun samu bugun tazarar yadi 30, amma daga bisani, Jamie Verdy ya farke kwallon a miniti na 56 kafin Sturridge ya zura tasa.

Yanzu haka dai Ingila ce ke saman teburi a rukuninsu na B.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.