An karrama 'yan wasan Albania
Al’ummar kasar Albania sun karrama ‘yan wasan tawagar kwallon kafa ta kasar duk da cewa an fitar da su daga gasar cin kofin kasashen Turai da ake gudanarwa a Faransa.
Wallafawa ranar:
‘Yan wasan sun samu kyakkayawar tarba tamkar wadanda suka lashe kofin gasar bayan sun koma gida a jiya Alhamis.
A karon farko kenan a tarihi da kasar ta halarci irin wannan babbar gasar a duniya, kuma an bayyana ‘yan wasan a matsayin gwarzaye saboda nasarar da suka samu a kan Romania.
Gwamanatin kasar ta yi alkawarin bai wa ‘yan wasan Fasfo na Diflomasiya saboda abinda da suka yi na daga darajar kasar a idon duniya.
Sannan kuma gwamantin ta bai wa tawagar kwallon kafar karin kudi har Euro miliyan 1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu