Ibrahimovic zai koma Manchester United
Zlatan Ibrahimovic na Sweden ya bayayyana cewa, zai koma Manchester United domin ci gaba da taka leda, abinda ya kawo karshen jita-jitar da ake ta yi kan makomarsa.
Wallafawa ranar:
Dan wasan mai shekaru 34 da haihuwa zai fara taka leda a gasar Premier ta Ingila a kakar wasanni mai zuwa kuma shi ne mutun na biyu da Manchester United ta dauka a karkashin sabon kocinta Jose Mourinho bayan Eric Bailly na kasar Ivory Coast.
Ibrahimovic wanda ya taka leda a Paris St Germaine ta Faransa zai kulla kwantiragin shekara guda ne, inda zai rika karban Pam dubu 220 a kowanne mako a matsayin albashi kamar yadda kafafen yada labaran Birtanya suka rawaito.
Tuni dai Ibrahimovic ya yi ritaya daga buga wa kasara ta Sweden tamaula bayan sun gaza kai ga gaci a gasar cin kofin nahiyar Turai a Faransa kuma a jumulce ya ci wa kasar kwallaye 62 cikin wasanni 116 da ya buga ma ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu